Labaran Duniya
“DA ƊUMI-ƊUMINSA: Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Bada Sanarwar Ganin Watan Shawwal A Nijeriya


“DA ƊUMI-ƊUMINSA: Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Bada Sanarwar Ganin Watan Shawwal A Nijeriya
Daga Jamilu Sani Rarah Sokoto
Majalisar ƙoli mai kula da harkokin addinin musulunci ta Najeriya (NSCIA) ƙarƙashin jagorancin mai Alfarma sarkin musulmi Sultan Abubakar Saad CFR mni ta bada sanarwar tabbacin ganin watan Shawwal a Nijeriya.
A gobe Juma’a 21, ga watan Afrilu, 2023, shine ranar Sallah wanda shi ne zai kama 1, ga watan Shawwal na shekarar 1444.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Media Aide to Sultan of Sokoto