Labaran Duniya

Gwamnati ta yi gagawan hukunta Dr. Idris Abdul’razak – Kiran Sheikh Ɗahiru Bauchi.

  1. Gwamnati ta yi gagawan hukunta Dr. Idris Abdul’razak – Kiran Sheikh Ɗahiru Bauchi.de

 

Muna Goyon Bayan Gwamnati Ta Rushe Masallaci Da Makarantar wanda yake koyar da raini ga janibin Annabi (Su’ul Adab) hakkin tane Rushe wajan da ake koyar da rashin ladabi da yiwa Annabi Gatsali.

 

Fitaccen malamin addinin musulunci kuma jigon dariqar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana bara’arsa ga kalamai na cin fuska da Gatsali da wani mutum yayi ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam inda ya nemi da a gaggauta yanke masa hukunci, malamin yace irin wadannan mutane bama a zama dasu da sunan muƙabala sai dai tuhuma.

 

Shehin Malamin ya nuna hakan a matsayin kuskure inda ya ce wasu malamai sun tafi a kan haramcin yi wa Mu’utazilawa martani, domin kafin martanin sai an maimaita abin da suka fada wanda hakan shi ma kuskure ne balle kuma akan Manzon Allah (S.A.W).

 

Kayan Allah na Annabi ne bazai taɓa yiwuwa ace anci fuska ko yin Gatsali ga Annabi Sallallahu alaihi Wasallam da sunan fitar da hakkin Allah ba, wannan su’ul Adab ne ga Annabi kuma hukunta duk wanda yayi wajibi ne ga gwamnati.

 

Allah Ya Kara wa Sheikh Dahiru Uthman Bauchi Lafiya da Tsawon Kwana Mai Anfani, Allah Ya Kara Mana Imani Mu Cigaba da Samun Taimakon Allah Alfarman Manzon Allah (SAW).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button