Labaran Duniya

Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un Kalli Bidiyon Yadda ‘Yan Dana Suka Mamaye Rumfunan Zaɓe A Legos Sun Ban Kawa Akwatin Zabe Wuta….

‘Yan daba da dama sun yiwa wasu rumfunan zabe kawanya a yankin Oshodi da Itire dake Legas inda suka banka wa wasu takardu da akwatuna wuta.

/ Siyasa
‘Yan daba sun mamaye rumfunan zabe a Legas

Wallafawa ranar: 25/02/2023 – 14:23

Mutane sun yi jerin gwano yayin da suke jiran motar bas ta BRT a gundumar Ojota a birnin Legas,
Mutane sun yi jerin gwano yayin da suke jiran motar bas ta BRT a gundumar Ojota a birnin Legas, © REUTERS/Akintunde Akinleye
Zubin rubutu:
Abdoulaye Issa
Minti 1
‘Yan daba da dama sun yiwa wasu rumfunan zabe kawanya a yankin Oshodi da Itire dake Legas inda suka banka wa wasu takardu da akwatuna wuta.

TALLA
‘Yan daba wadanda dukkansu sanye da bakaken kaya da rufe fuska, sun isa yankin ne da misalin karfe 11:30 na safiyar yau asabar.

Wasu masu kada kuri’a, wadanda ba su iya guduwa ba lokacin da ‘yan daba suka iso sun ji rauni.

Majiyoyi sun ce ‘yan daba, daga baya sun zagaya yankin, mintuna kadan bayan wasu jami’an tsaro da ke aikin zabe sun bar aikinsu.

A cewar Tajudeen Haruna, bayan mintuna kadan ne ‘yan daba suka bude wuta tare da tsorata masu kada kuri’a.

“Daga baya ne ‘yan daba suka cinna wa akwatin zabe da wasu kayayyaki wuta,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button