Labaran Duniya

Innalillahi Wainna ilaihirrajiun Allah Yayiwa Shehin Malamin Addinin Musulunci dake Zaune a Kaduna, Rasuwa

Innalillahi Wainna ilaihirrajiun Allah Yayiwa Shehin Malamin Addinin Musulunci dake Zaune a Kaduna, Shaikh Hamza Muhammad Lawal rasuwa

Jaridar Rariya Hausa ta ruwaito Rahoton rasuwar Sheikh Hamza Mohd Lawal Kamar haka ” Rahotannin dake shigowa Jaridar RARIYA a halin yanzu na nuni da cewa Shehin Malamin nan na addinin Musulunci dake zaune a Kaduna, Shaikh Hamza Muhammad Lawal Badikko ya rasu.

Bayanai daga makusantan Shehin Malamin sun tabbatar da labarin rasuwar Malamin. Sai dai ba su fayyace wa majiyarmu yadda Shehin Malamin ya rasu ba kuma yaushe ba.

Ya zuwa hada takaitaccen rahoton nan, babu wata sanarwa a hukumance daga iyalan mamacin ko makusantansa kan rasuwarsa.”

Muna masa Addu’a Allah Yaji kanshi da rahama idan tamu tazo yasa mu cika da kyau da imani ameen.

Mungode da ziyarar wanna shafin namu mai al’barka domin samun labarai masu ingance akoda yaushe mungode da ziyarar wanna shafin namu mai al’barka.

www.fotisify.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button