Kannywood

Jarumi Adam Zango Ya Saki Matarsa bayan shafe watanni ana dambarwa a tsakanin su.

Jarumi Adam Zango Ya Saki Matarsa bayan shafe watanni ana dambarwa a tsakanin su.

Bayan kwashe watanni bata gidansa bisa yajin da ta yi, daga karshe dai aureņ jarumin Kannywood Adam A. Zango ya mutu da matarsa Safiyya Umar Chalawa.

Sai dai duk da cewa ba saki uku ya yi mata ba, amma majiyarmu ta Mujjalar Fim ta ruwaito tun can akwai saki daya a tsakaninsu tun ta na amarya, yanzu kuma ya sake aika mata da na biyu a gidansu da ke Birnin Kebbi.

A farkon wannan shekarar ne Adam Zango ya sanarwa duniya yiwuwar rabuwarsu da Saffiyya bisa abin da ya kira da “kin bin umarninsa” da ta ke yi bayan ya gano tana wani kasuwancin intanet kuma ya hanata ta ki hanuwa.

Wannan shi ne auren jarumin na shida da ya mutu tsakanin shekarar 2006 da ya yi auren fari zuwa wannan shekarar.

Yanzu dai yana da yara bakwai uku mata hudu maza, wadanda kowanne daga cikinsu mahaifiyarsa daban.

Source: Dokin Ƙarfe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button