Kannywood
Lauyoyi A Kano Sun Kai karar Mawaki Rarara Wajen Sarkin Katsina da Sarkin Daura….


Wasu rukunin lauyoyi a nan Kano sun yi karar Mawakin nan Dauda Kahutu Rarara wajen Maimartaba Sarkin Katsina da Maimartaba Sarkin Daura.
A takardar da suka aike wa Sarakunan sun bayyana kokensu kan zargin Rarara da yin wakoki yana aibata manyan yan siyasar jihar Kano.
Sannan wakokin suna janyo zage-zage da cin zarafi a tsakanin jama’a.
Lauyoyin sun kuma ba wa Rarara shawarar ya gyara harshensa a gaba, sannan ya fito ya nemi afuwa ko kuma su dauki mataki na gaba.
Barr. Badamasi Sulaiman Ganduje shi ne jagoran wadannan lauyoyi ya yi karin bayani a kai.