SANARWA DAGA KUNGIYAR IZALA AKAN MUKABALA DA MALAM IDRIS


- SANARWA DAGA KUNGIYAR IZALA AKAN MUKABALA DA MALAM IDRIS
Daga birnin Dutsen jihar Jigawa, inda shugaban Majalisar Malaman kungiyar Izala na jihar Bauchi bangaren Jos Sheikh Salihu Suleman Ningi yake gabatar da tafsirin Al-Qur’ani Maigirma yanzu haka, ya fitar da sanarwa akan mukabalar da hukumar shari’ah na jihar Bauchi ta shirya za’ayi da Sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Bauchi.
Sheikh Salihu Suleman Ningi yace babu hannun kungiyar Izala da yake jagoranci a cikin wannan zaman, kuma babu wani dan Izala da zai halarci zaman mukabala da Malam Idris akan abinda ya tabbata gaskiya ne a Sunnah
Malam yace duk wani dan Izala reshen Jos da aka gani gurin mukabalar ya je ne a kashin kansa ba da yawun kungiya ba, kamar yadda wasu suka fadawa Malam Idris cewa ‘yan Izalar Jos zasu shiga cikin ‘yan bidi’ah da zasuyi mukabala dashi, to ba gaskiya bane
Sannan a bangaren Izala reshen Kaduna jihar Bauchi, Sheikh Dr Ibrahim Disina yace Izalar Bauchi ta wakiltashi zasu halarci mukabalar domin su goyi bayan Sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Bauchi
Gobe taron dangin ‘yan bidi’ah da zindikai a jihar Bauchi zasu kwashi kashinsu a tafin hannu da ikon Allah
Yaa Allah Ka daura gaskiya akan karya, Ka taimaki sunnah akan bidi’ah da shirka