Labaran DuniyaNewsTechnology

Wasu ƴan bindiga sun kai hari kan garin Jangebe da ke Ƙaramar Hukumar Talatar Mafara a jihar Zamfara Kalli wannan video innalillahi wainna ilaihi Raju un karka bari abaka labari…

Wasu ƴan bindiga sun kai hari kan garin Jangebe da ke Ƙaramar Hukumar Talatar Mafara a jihar Zamfara, inda bayanai suka ce sun kashe mutane tare da yin garkuwa da wasu.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu shi ne wani sanannen likita, sannan kuma ƴan bindigar sun yi garkuwa da yariman garin.

Dan uwan likitan wanda ya zanta da BBC, ya ce ƴan bindigan sun je gidan likitan ne da misalin ƙarfe 12 na dare.

Ya ce “suna zuwa gidan sai suka harbe shi, harbi huɗu suka yi mashi.”

Ya kuma ce ƴan bindigan sun tafi da matan marigayin biyu da yara huɗu.

Baya ga wannan, a yankin Shinkafi kuma ƴan bindiga sun buɗe wa wasu daliban makarantar Islamiya wuta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button