Labaran Duniya

Yadda Aka Cika Makil A Wajen Rufe Tafsirin Kur’ani Da Young Sheik Ke Gabatarwa A Garin Zaria

Yadda Aka Cika Makil A Wajen Rufe Tafsirin Kur’ani Da Young Sheik Ke Gabatarwa A Garin Zaria

A yinin yau Laraba 28 ga watan Ramadan, wanda ya yi daidai da 19 ga watan Aprilu 2023, Muhammad Zakeer Shamsudeen Ali Mai Yasin, wanda aka fi sani da Young Sheikh Zaria ya rufe tafsirin Qur’ani mai girma na wannan shekara.

Wannan rufe tafsir na yau shine karo na uku da Sheikh din ya gabatar.

Dimbin jama’a maza da mata yara da manya ne suka halarta, Malamai na addini da malamai daga manyan makarantun zamani da Sarakuna iyayen al’umma manyan gidajen jaridu a Najeriya duk sun halarci rufewar.

Bayan kammala karatun an yi tambayoyi, inda shi kuma Sheikh din ya bayar da amsa.

 

Young Sheikh dai karatuttukan sa yana cikin wanda yake daukan hankali da kuma tattaunawa akai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button