Labaran Duniya
Yadda nike amfani da yatsun ƙafa wajen Rubutu da Alwala sakamakon rashin hannuwa—Maryam Umar


Maryam Umar ‘yar shekara 22 daga jihar Gombe, wadda aka haifa ba ta da hannuwa ba, ta ƙara da cewar “Na sami ƙwarewar yin amfani da yatsun ƙafata a zahiri, kuma na yi imani cewa baiwa ce daga Allah.
Na fara amfani da ƙafata wajen rubutawa tun ina ƴar shekara uku kacal, ba tare da wani ya koya mani yadda zanyi amfani da ƙafata ba. Ina danganta wannan ikon da shiriyar Allah da falalarsa. Da kafafuna na iya yin ayyuka daban-daban kamar su wanke tufafi, shafa ruwan alwala, goge hakora, da yin alwala a matsayina na mace musulma, har ma da shafa kayan shafa don kara min kyawu.