Labaran Duniya

Yanzu Yanzu Dai dai lokacin da hukumar INEC ke ci gaba da tattara sakamakon zabe a Najeriya, wasu jam’iyyu sun fice daga dakin tattara sakamakon zaben

Dai dai lokacin da hukumar INEC ke ci gaba da tattara sakamakon zabe a Najeriya, wasu jam’iyyu sun fice daga dakin tattara sakamakon zaben saboda zargin hukumar da kin sanya sakamakon a rumbunan adana bayananta, yayinda a bangare guda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ke kira da soke zaben wasu yankunan kasar batuun da tuni gwamnatin Tarayya ta gargade shi kan yunkurin tayar da hankula.
Yaya kuke kallon wannan dambarwa ?
Kuna ganin INEC ta sabawa alkawarin da ta dauka?
Kun goyi bayan soke zaben da wasu ke bukata?
Wanne fata kuke da shi don samun mafita?
Muna dakon ra’ayoyinku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button