Labaran Duniya

Yanzu yanzu kotu ta aika da Alhassa ado doguwa zuwa gidan yari kalli wannan video innalillahi wainna ilaihi raju’un…

Wata kotun majistare a jihar Kano ta aike da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya Alhassan Ado Duguwa zuwa gidan yari bayan gurfanar da shi a gaban kotun.

Ana zargin ɗan majalisar da muggan laifuka ciki har da zargin aikata kisan kai da mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba da hannu a kunna wuta a wani gini.

An gurfanar da shi tare da wani mutum wanda ake zargi sun haɗa baki wajen aikata kisan kai da tayar da zaune-tseye a ƙaramara hukumar Tudun wada da ke jihar ranar Asabar da ta gabata.

Alƙalin kotun ya ɗage shari’ar zuwa ranar 7 ga watan Maris domin duba buƙatar yiyuwar bayar da belin ɗan majalisar ko kuma akasin haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button