Kannywood

Yanzu Yanzu Kotu Ta Yankewa Murja Ibrahim Hukuncin Zuwa Gidan gyaran Hali Kalli Vedion……

Yanzu Yanzu nan Kotu Shari’ar Musulunci dake kano ta tisa keyar Murja ibrahim kunya izuwa gidan gyaran Hali.

Wata Kotun shari’ar Muslunci dake a Jahar Kano ta tisa keyar fitacciyar Jarumar TikTok dinnan watau Murja Ibrahim Kunya izuwa gidan ajiya da gyaran hali sakamakon tuhume tuhume hade da kalaman batsa, da take yi a shafukan ta na sada Zumunta Musamman ma na TikTok.

Kamar dai yadda aka sani acikin makon nan da muke ciki ne Yan sandan jahar kano suka kama Murja ibrahim kunya adaidai lokacinda take kokarin shirya wani gagarumin Shagalin Bikin Ranar Zagayowar Haihuwar ta.

Murja Zata shirya wannan birthday ne a ranar lahadin data gabata wanda kuma hakan bata samu ba inda aka kamata a ranar Asabar.

Wata kungiya ce ta malaman Addinin Musulunci suka kai kararta inda suke tuhumar ta dayin abubuwa wanda suka shafi zage zage, Kalaman batsa, raye raye na rashin da’a da dai sauran su.

A Zantawar da yan sanda sukayi da ita, Murja ta amsa wasu daga cikin laifukan da ake tuhumar ta, indama ta bayyana cewa Zage zagen da takeyi yana daya daga cikin kalubalen da take fuskanta kuma Insha’Allahu ba zata kara ba.

Hakan yasa ma kotu ta bukaci da akaita Asibitin kwakwalwa domin duba Lafiyar ta, sai dai kamar abu ya lafa kawai sai mukaji cewa kotu ta aika da ita izuwa gidan gyaran hali Kamar yadda jaridar Alfijir hausa suka ruwaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button